Isa ga babban shafi
Wasanni

An gaza gano jirgin Emiliano Sala na Cardif City da ya yi batan dabo

Jami'an tsaron Faransa sun dakatar da aikin laluben jirgin dan wasan gaba na Nantes Emiliano Sala da ya bace tun da yammacin jiya Litinin akan hanyarsa ta zuwa Birtaniya don fara taka leda a Cardiff City aiki bayan sauya sheka a Asabar din makon nan.

Tun a yammacin jiya litinin ne Emiliano Sala ya yi batan dabo lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Ingila don fara taka leda a Cardif City.
Tun a yammacin jiya litinin ne Emiliano Sala ya yi batan dabo lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Ingila don fara taka leda a Cardif City. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Sala wanda ke matsayin dan wasa mafi tsada da Cardiff ta saya a safiyar yau ne yakamata ace ya fara atisaye da sabon Club din nasa inda ya yi bankwana da tsohon Club dinsa tun a jiya Litinin.

Fiye da sa’o’I 30 kenan jami’an na aiki ta hanyar amfani da jiragen ruwa da kuma na sama amma sun gaza gano jirgin wanda ke dauke da mutane biyu kacal wato Sala da kuma Piper Malibu matukin jirgin.

Emiliano Sala mai shekaru 28 wanda Cardiff ta sayo daga Nantes ta faransa kan yuro miliyan 17 a wannan kakar kadai ya zura kwallaye 13 a bangaren Nantes.

Hukumomin Cardiff dai sun ce basu yarda cewa dan wasan mutuwa yayi ba inda suke fatan gano shi da ransa, yayinda can a Faransa kuwa tuni magoya bayan dan wasan suka fara makoki yayinda tsohon Club din nasa ya dakatar da wasansa na gobe da zai kara da Etente SSG don nuna alhini da batan dan wasan.

Jami’an da ke aikin laluben jirgin na Cardiff dai sun ce ko da ace jirgin nutsewa ya yi a ruwa iyakar lokacin da za su dauka a rage shi ne wadannan sa’o’in.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.