Isa ga babban shafi
wasanni

Kungiyoyin Ingila na fatarar maciya kwallaye

Kusan rabin manyan kungiyoyin Ingila da ke buga gasar firimiyar kasar, na bukatar sayen masu zura kwallaye a raga lura da fatarar jefa kwallayen da suke fama da ita a wannan kaka.

Kungiyoyin Ingila da dama sun gaza zura kwallaye masu yawa a kakar bana
Kungiyoyin Ingila da dama sun gaza zura kwallaye masu yawa a kakar bana REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Kungiyoyin na neman siraikokin da za su cilla su can saman teburi ko kuma akalla su kubutar da su daga karewa a matakin ‘yan dagaji.

Tuni Bournemouth ta shiga kasuwa, inda ta yi cefanen dan wasan Ingila mai doka kwallo a tawagar ‘yan kasa da shekaru 21, wato Dominic Solanke akan Pam miliyan 19, yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa, nan gaba Chelsea za ta sayi dan wasan gaba na Bournemouth, wato Callum Wilson da darajarsa ta kai Pam miliyan 50.

Kungiyoyin da za ace, sun fi bukatar ‘yan wasan gaba sun hada da Huddersfield da Fulham da Newcastle. Sai kuma Cardiff da Southampton da Burnley da Crystal Palace.

Wadannan kungiyoyi bakwai na fatarar ruwan bala-balai a raga, abin da ya jefa su kasan teburin gasar firimiyar Ingila.

A bangare guda, rahotanni na cewa, Manchester United za ta raba gari da Marouane Fellaini dan asalin Belgium, in da take tsammanin karbar Pam miliyan 15 a matsayin farashinsa.

Ana ganin AC Milan da Porto har ma da Guangzhou ta China, dukkaninsu sun nuna sha’awar sayen Fellaini din da zaran Manchester United ta rabu da shi.

Har ila yau, Chelsea, na burin samun ci gaba a yarjejeniyar kulla kwantigi da dan wasan gaba na Juventus, Gonzalo Higuain, wanda yanzu haka ke take leda a AC Milan, amma akan aro.

Wa’la'alla a kammala yarjejeniyar sayen Higuain din a karshen wannan mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.