Isa ga babban shafi
wasanni

Salah ya shirya sake lashe kyautar gwarzon Afrika

Gwarzon dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya shirya tsaf don sake lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afrika  karo na biyu a jere a wani gagarumin biki da zai gudana a Senegal a ranar Talata.

Pierre-Emerick Aubameyang da Sadio Mané da Mohamed Salah
Pierre-Emerick Aubameyang da Sadio Mané da Mohamed Salah Photos Reuters/David Klein-Carl Recine-Lee Smith _ Montage RFI
Talla

Salah dan asalin Masar na takarar lashe wannan kuyata ce da abokin taka ledarsa a Liverpool, wato Sadio Mane na Senegal da kuma Pierre-Emerick Aubameyang  dan asalin Gabon da ke taka leda a Arsenal.

A bara, Salah ya jefa kwallaye 44 a wasanni daban daban da ya buga wa Liverpool, yayin da yake ci gaba da taka rawa iya gwargwado a kakar bana.

Muddin ya sake lashe kyautar a yau Talata, to Salah zai kasance dan wasa na farko daga arewacin Afrika da daya lashe kyautar sau biyu a jere.

Wata Mujallar Kwallon Kafa ta Faransa ce ta fara bayar da wannan kyauta ta Ballon d’Or a Afrika shekaru da dama da suka shude kafin daga bisani ta mika ragama ga Hukumar CAF a tsakan-kanin shekarun 1990.

A bangare guda, duk a ranar Talatar ce Hukumar Kwallon Kafar Afrika za ta zabi kasa daya tsakanin Masar da Afrika ta Kudu don ba ta izinin karbar bakwancin gasar cin kofin nahiyar ta 2019.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar ta janye izinin gudanar da gasar daga hannun Kamaru a cikin watan Nuwamba saboda tsaikon da kasar ke samu wajen tanade-tanaden gasar da kuma barazanar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.