Isa ga babban shafi
Wasanni

Solskjaer ya kare salon horarwarsa a United

Sabon kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce salon horarwarsa bai dogara kan gina ‘yan wasansa wajen neman zura kawallaye da yawa kawai ba.

Sabon mai horar da kungiyar Manchester United Ole Gunnar Solskjaer.
Sabon mai horar da kungiyar Manchester United Ole Gunnar Solskjaer. REUTERS / Marcelo del Pozo
Talla

Solskjaer ya bayyana haka ne lokacin da yake kare kansa daga sukar wasu da ke cewa, yafi mayar da hankali wajen bin tsarin zari ruga domin samun nasara a wasannin da yake jagorantar United, la’akari da cewa ba shi da kwarewa gina karfi da kwarewar ‘yan wasa ta kowane fanni.

Jim kadan bayan wasan da United ta lallasa FC Bournamouth da kwallaye 4-1, Solskjaer ya ce yana gina ‘yan wasa kan dukkanin fannonin da wasan kwallon kafa ke bukatar kwarewa na tsare gida, kasafta kwallo dalla dalla kafin jefa ta a ragar abokan karawa.

Yayin fafatawar gasar Premier ta ranar Lahadi, Paul Pogba ne ya ci wa United kwallaye biyu yayin da Rashford da Lukaku suka jefa sauran.

Bayan sallamar tsohon kocinsu Mourinho, United ta samu nasarar cin kwallaye 12 a wasanni uku kawai, yayin da aka jefa mata uku kacal.

A halin yanzu tazarar maki uku kawai ya rage tsakanin Manchester United da ke matsayi na shidda da maki 35, da kuma Arsenal da ke mataki na biyar a gasar Premier da maki 38.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.