Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid na kokarin sake daukar Mourinho - El Pais

Tsohon mai horar da Manchester United Jose Mourinho, ya ce yana matukar alfahari da lokacin da ya shafe yana horar da kungiyar kafin korar shi da ta yi daga bakin aiki.

Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. REUTERS/Pedro Nunes
Talla

Sai dai cikin sanawar da ya baiwa manema labarai a Birtaniya, Mourinho ya kaucewa yin tsokaci kan dalilan da suka jawo korar ta shi da kungiyar ta yi, sa’o’i bayan lallasa United da Liverpool ta yi da kwallaye 3-1 a gasar Premier.

Tuni dai United ta maye gurbin Mourinho da tsohon dan wasanta Ole Gunnar Solskjaer wanda zai ci gaba da rikon kwaryar horar da ‘yan wasanta zuwa lokacin da za ta dauki sabon koci na dindindin.

Bayan wasanni 17 dai Liverpool da ke jagorantar gasar Premier, ta baiwa Manchester United tazarar maki 19.

To sai dai masu iya magana sun ce “abincin wani gubar wani”, zalika “abin rabo ne kuturu ya kama tarwada”, domin kuwa jim kadan bayan korar Mourinho da Manchester United ta yi, rahotanni sun ce, Real Madrid na shirin sake daukarsa domin farfado da karsashinta.

Jaridar El Pais da ke Spain ta rawaito cewa, zuwa yanzu karo na biyu kenan a wannan kakar wasa, da shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez ke yi wa Mourinho tayin komawa garesu, domin sake gina karfin ‘yan wasan kungiyar.

Jaridar ta kara da cewa Perez ya yi wa Mourinho tayin albashin euro miliyan 18 a shekara ba tare da haraji ba, zalika ya yi alkawarin baiwa Mourinho damar zama shugaba mai cikakken iko dangane da saye da sayarwar ‘yan wasan kungiyar da yake da bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.