Isa ga babban shafi
wasanni

An fitar da sabon jadawalin gasar zakarun Turai

An fitar da jadawalin kungiyoyi 16 da za su ci gaba da fafatawa da juna a gasar zakarun nahiyar Turai a ranar Litnin a birnin Nyon na Switzerland.

Za a fara zagayen farko na matakin kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turan a cikin watan Fabairun badi
Za a fara zagayen farko na matakin kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turan a cikin watan Fabairun badi FRANCK FIFE / AFP
Talla

Schalke 04 za ta hadu da Manchester City, sai Atletico Madrid da za ta kara da Juventus, yayin da Manchester United za ta fafata da Paris Saint-Germain.

Tottenham za ta hadu da Borussia Dortmund kamar yadda Lyon za ta kai ruwa rana da Barcelona, sai kuma Roma da Porto, da kuma Ajax wadda za ta barce gumi da Real Madrid mai rike da kambin gasar.

Kungiyoyin da suka kammala a mataki na biyu a teburin jadawalin farko, sune za su fara karbar bakwancin wasannin farko a ranakun 12 da 13 da kuma ranakun 19 da 20 ga watan Fabairu mai zuwa kafin a gudanar da zagaye na biyu a ranakun 5da 6 da kuma 12 da 13 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.