Isa ga babban shafi
Wasanni

Salah ya kafa sabon tarihi a gasar Premier

Muhammad Salah ya sake kafa tarihi a Liverpool, bayan da ya ci wa kungiyar tasa kwallaye 3 a wasan gasar Premier da suka fafata a karshen mako, wanda suka lallasa Bournemouth da kwallaye 4-0.

Muhammad Salah na kungiyar Liverpool yayin fafatawa da kungiyar Bournemouth.
Muhammad Salah na kungiyar Liverpool yayin fafatawa da kungiyar Bournemouth. REUTERS/Peter Nicholls
Talla

Kwallayen uku na Salah, sune cikon na 40 da ya ci wa Liverpool a wasanni 52 da ya buga mata, abinda ke nuni da cewa shi ne dan wasan kungiyar na farko da ya ci kwallaye masu yawa cikin wasanni kalilan.

A gefe guda kuwa, kwallaye ukun na Salah, sune na farko da wani dan wasan Liverpool ya ci, yayin da suka yi tattaki zuwa gidan wata kungiya, tun bayan irin bajintar da Luiz Suarez yayi a kungiyar cikin shekarar 2014.

A bangaren tarihin gasar Premier kuwa, Alan Shearer da Andy Cole ne kawai suka samu nasarar zarta Muhammad Salah ta hanyar cin kwallaye 40 cikin wasanni 45.

Tun bayan soma kakar wasan manyan gasannin nahiyar turai guda 5 a bara, Lionel Messi ne kawai ya zarta Salah wajen yawan kwallaye da 43, yayinda dan wasan na Liverpool ke da 42, sai kuma Harry Kane na Tottenham da kwallaye 39.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.