Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Ronaldo ya kalubalanci Messi kan ya sauya sheka daga Barcelona

Dan wasan gaba na Juventus, Cristiano Ronaldo ya kalubalanci takwaransa na Barcelona Lionel Messi kan sauya sheka zuwa daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar Italiya kamar yadda ya yi.

Ronaldon wanda ya gwada sa’arsa a Ingila da Spain yanzu kuma ya ke taka leda a Italiya ya ce ya karbi kalubale wajen sauya sheka kuma ya na fatan Messi ma zai karba.
Ronaldon wanda ya gwada sa’arsa a Ingila da Spain yanzu kuma ya ke taka leda a Italiya ya ce ya karbi kalubale wajen sauya sheka kuma ya na fatan Messi ma zai karba. AFP
Talla

Ronaldo mai shekaru 33 ya ce yana fata watarana Messi ya sauya ra’ayinsa na kare kwallon kafarsa a Spain don gwada wani bangare na duniya daban, a cewarsa ta hakan ne za a kara gane kwazonshi.

Ronaldo da Messi mai shekaru 31 wadanda suka shafe tsawon kusan shekaru 10 suna lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or har yanzu na a matsayin ‘yan wasa biyu da babu kamarsu a duniyar kwallo.

Sai dai Ronaldon dan Portugal wanda ya koma Juventus daga Madrid kan yuro miliyan 99 a wannan kaka bayan shafe shekaru 9 a Spain, ya ce sai dan wasa ya gwada sa’ar sa a kungiyoyi daban-daban ne za a gane kwazon a tare da shi ne ba wai a tare da kungiyar sa ba.

Ronaldon wanda ya gwada sa’arsa a Ingila da Spain yanzu kuma ya ke taka leda a Italiya ya ce ya karbi kalubale wajen sauya sheka kuma ya na fatan Messi ma zai karba, amma idan har yana farin ciki a Barcelonar sa kamar yadda ya ke yi a baya, to yana masa fatan alkhairi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.