Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool za ta iya lashe gasar Firimiya ta bana - Guardiola

Masu sharhi kan al’amuran wasanni na ci gaba da tsokaci kan kalaman mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola da ke nuna cewa Liverpool ka iya lashe kambun Firimiya a wannan kaka.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

A tattaunawar da aka yi da shi bayan shan kayensu hannun Chelsea da kwallaye 2 da banza cikin karshen makon nan, Guardiola ya ce rawar da Liverpool ke takawa a wannan kaka na nuni da za ta iya karbe kanbun daga hannunsu.

Bayan nasarar Liverpool kan Bournemouth da kwallaye 4 da banza ana ganin Club din ya tattara karfin sa ne a gasar Firimiya bayan fitar da shi daga gasar zakarun Turai da PSG ta yi makon jiya.

Yanzu haka dai Liverpool ce saman teburin Firimiya da maki 42 tazarar maki 1 kacal da Manchester City da ke matsayin ta biyu, wanda kuma masu sharhin ke cewa rabon da a samu irin wannan tazara a Firimiya tun a kakar wasa ta 2010-2011 tsakanin Manchester United da Arsenal.

Haka zalika rabon Liverpool da kaiwa wannan mataki da makamancin makin tun a kakar wasa ta 1996-1997 fiye da shekaru 20 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.