Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea ta sanya farashin euro miliyan 12 kan Moses

Kungiyar Chelsea ta sanya farashin euro miliyan 12 kan dan wasanta Victor Moses, biyo bayan tayin sayensa da Crystal Palace ta yi.

Victor Moses yayin fafata wasa tsakanin Chelsea da Southampton a filin wasa na Stamford Bridge. 25/4/17.
Victor Moses yayin fafata wasa tsakanin Chelsea da Southampton a filin wasa na Stamford Bridge. 25/4/17. Reuters / John Sibley Livepic
Talla

Moses dan Najeriya mai shekaru 27, yana fuskantar kalubalen yawaitar zaman benci bayan zuwan sabon kocin Chelsea Maurizio Sarri, inda zuwa yanzu wasanni 6 kawai ya bugawa kungiyar a karkashin sabon mai horarwar.

Victor Moses wanda ya fi samun karbuwa a zamanin Antonio Conte, ya bugawa Chelsea wasanni 40 a kakar wasa ta 2016/2017 wadda cikinta ta daga kofin gasar Premier, yayinda a kakar wasa ta bara ya bugawa kungiyar wasanni 38.

A shekarar 2012, Chelsea ta sayi Moses daga kungiyar Wigan kan kudi fam miliyan 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.