Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Nasan zan fuskanci kalubale a Chelsea - Sarri

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Maurizio Sarri ya ce ya san cewar zai fuskanci kalubale sosai a kungiyar, duk da yadda suka fara kakar bana da tarin nasasrori.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Maurizio Sarri.
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Maurizio Sarri. www.mirror.co.uk
Talla

Sari na bayyana haka ne yayin da su ke shirin karawa da Manchester City a karshen wannan mako, wasan da ke da matukar tasiri ga kungiyar.

Chelsea ta buga wasanni 12 a jere babu wanda ya samu nasara akan ta, kafin shan kayen da ta yi ranar laraba a hannun kungiyar Wolves, abinda ya mayar da ita matsayi ta 4 da maki 31.

Ita kuwa kungiyar Manchester City har yanzu babu wanda ya samu nasara akan ta, yayin da take matsayin farko da maki 41.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.