Isa ga babban shafi
Wasanni

Haramcin shiga wasannin motsa jiki zai ci gaba da aiki akan Rasha

Hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF, ta sake tabbatar da hukuncin haramtawa hukumar wasannin motsa jikin Rasha RUSAF, shiga gasannin da take shiryawa.

Shugaban hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF Sebastian Coe (hagu) tare Rune Andersen, shugaban kwamitin hukumar ta IAAF kan ladabtar da kasar Russia, yayin taro a birnin Vienna, dake Austria.
Shugaban hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya IAAF Sebastian Coe (hagu) tare Rune Andersen, shugaban kwamitin hukumar ta IAAF kan ladabtar da kasar Russia, yayin taro a birnin Vienna, dake Austria. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Tun a shekarar 2015 Rasha ta fuskanci haramcin shiga wasannin, bayan wani rahoto da hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari tsakanin masu motsa jiki WADA ta wallafa, da ya bankado cewa gwamnatin Rasha na goyon bayan 'yan wasan kasar, wajen shan kwayoyin.

Tun daga waccan lokacin ne aka haramtawa masu wasannin motsa jikin kasar ta Rasha shiga gasanni da sunan wakilcin kasarsu, sai dai a matsayin ‘yan wasa masu cin gashin kai.

Kafin cimma burin dage mata haramcin, tilas Rasha ta amince da rahoton hukumar yaki da shan kwayoyin karin kuzari ta WADA, da ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na da hannu wajen taimakawa ‘yan wasanta saba ka’idar wasannin na motsa jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.