CAF ta gabatarwa da Afrika ta Kudu tayin ne cikin gajeren wa’adi bayan daukar matakin kwace damar da ta baiwa Kamaru a karkashin shugabancin tsohon shugaban hukumar ta CAF Isa Hayatou.
A halin yanzu ana dakon shawarar da kasar zata yanke idan aka gana tsakanin gwamnatin Afrika ta Kudu da kuma hukumar kula da kwallon kafar kasar.
A cewar CAF, ta dauki matakin ne a dalilin rashin gamsuwa da shirin kasar Kamaru na kammala ayyukan karbar bakuncin gasar.
Za’a soma gasar kwallon kafar ta nahiyar Afrika daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli, bayan sauya lokacin gudanar da gasar na watannin Janairu da Fabarairu.
A karon farko dai kasashe 24 ne za su fafata a gasar mai zuwa, sabanin guda 16 da aka saba gani.