Wright, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan matakin Emery ya dauka na ajiye Ozil a benci yayin wasan ranar Lahadin nan da Arsenal ta samu nasara kan Bournemouth da kwallaye 2-1.
Mesut Ozil ne dan wasan dake kan gaba wajen albashi mai tsoka a Arsenal inda yake amshe Fam dubu 350,000 a kowane mako.
Matakin hutar da Ozil dai kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito na da nasaba da gazawarsa wajen taimakawa kungiyar yadda ya kamata a wasanni uku da suka buga jere da juna inda suka yi canjaras a dukkaninsu.