Isa ga babban shafi
Wasanni

Sevilla ta karbe ragamar jagorancin gasar La liga

Kungiyar Sevilla ta dare saman teburin gasar la liga ta Spain a jiya Lahadi, bayan samun nasara kan Real Valladolid da 1-0.

Wasu 'yan wasan kungiyar Sevilla.
Wasu 'yan wasan kungiyar Sevilla. REUTERS/Murad Sezer
Talla

Sevilla ta tsinci wannan dami a kala ne, bayan da manyan kungiyoyin dake gasar ta La liga suka gaza samun nasara a wasanninsu na wannan karshen mako, da suka hada da Real Madrid, Atletico Madrid da kuma Barcelona.

A ranar Asabar dinnan Real Madrid ta sha kaye na bazata a hannun kungiyar Eiber da kwallaye 3-0, abinda yasa wasu ke digar ayar tambaya kan cewa anya ‘yan wasan kungiyar basa bukatar garambawul kuwa, anya Julen Lopetegui da aka kora a baya na da laifi?

A dai wasannin gasar ta La Liga na karshen mako aka fafata tsakanin Atletico Madrid da Barcelona inda aka tashi kunnen doki wato 1-1.

A halin yanzu Sevilla ke jagorantar gasar La Liga da maki 26, Barcelona na biye da maki 25, sai kuma Atletico Madri da maki 24.

Kungiyoyin Alves mai maki 23 da Espanyol mai maki 21, ke a matsayin na 4 da na 5, yayinda Real Madrid ke biye musu da maki 20 a kan matsayi na 6.

Rabon da kungiyar Sevilla ta lashe kofin gasar La Liga tun a shekarar 1946.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.