Isa ga babban shafi
wasanni

Drogba ya yi ritaya daga buga kwallon kafa

Dan wasan Ivory Coast da ya taka leda a Chelsea, Didier Drogba ya sanar da ritayarsa daga buga kwallon kafa bayan shafe shekaru 20 cikin sana’ar taka leda.

Didier Drogba
Didier Drogba AFP PHOTO /FREDERIC J.BROWN
Talla

Drogba mai shekaru 40 ya jefa kwallaye 164 a wasanni 381 da ya buga wa Chelsea, yayin da ya lashe kofin firimiyar Ingila sau hudu da kofin FA hudu da kuma kofin gasar zakarun Turai a shekarar 2012.

Kazalika gwarzon dan wasan ne ke kan gaba wajen yawan kwallaye a kasarsa ta Ivory Coast, in da ya jefa kwallaye 65 a wasannin kasa da kasa.

Drogba ya taka leda Klub Klub daban daban tsakanin kasashe 6, amma ya fi samun nasarori a Ingila da Faransa.

A baya-bayan nan, Drogba ya taka leda a Phoenix Rising da ke Amurka, kuma daga wannan kungiya ce ya rataye takalmansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.