Isa ga babban shafi
Wasanni

Southgate ya bukaci 'yan wasan Ingila su karrama Rooney

Mai horar da ‘yan kwallon kafa na Ingila Gareth Souhgate, ya ce akwai bukatar ‘yan wasansa su san tarihin gudunmawar da tsohon dan wasa Wayen Rooney ya baiwa kasar, domin su rika mutunta.

Wayne Rooney, tsohon dan wasan kasar Ingila.
Wayne Rooney, tsohon dan wasan kasar Ingila. Reuters / Stefan Wermuth Livepic
Talla

Gareth Southgate ya bayyana haka ne yayin da yake maida martani kan sukar shi da wasu ke yi kan matakinsa na gayyatar Rooney domin bugawa Ingila wasan sada zumunci da Amurka a mako mai zuwa, wato ranar 15 ga watan Nuwamba.

A cewar kocin, an tsara wasan ne domin karrama dan wasan, zalika an yiwa wasan sada zumuncin taken “Rooney Foundation International”

Yayin wasan Rooney zai shiga fili ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, zalika ba zai rike mukamin kaftin ba, ba kuma zai sa riga mai lamba 10 da ya sabawa sanyawa Ingila ba.

Wasan dai zai zama karo na 120 da Rooney mai shekaru 33, zai bugawa kasarsa.

Rooney ya bugawa Ingila wasanni 119 inda ya ci kwallaye 53, wasa na karshe da ya bugawa Ingila shi ne wanda suka fafata da Scotland a watan Nuwamba na shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.