Isa ga babban shafi
Wasanni

Allegri na fatan Juventus ta dage kofin Serie A karo na 8

Kociyan Kungiyar kwallon kafar Juventus ta Italiya Massimiliano Allegri ya ce yana fatan Club din ya ci gaba da rike kambunsa na zakara a wasannin Serie A don samun damar dage kofin a jere karo na 8 a wannan kaka.

Wasan na Juventus da Man United shi ne karon farko da Juve ta sha kaye cikin fiye da watanni 5.
Wasan na Juventus da Man United shi ne karon farko da Juve ta sha kaye cikin fiye da watanni 5. Reuters/ Max Rossi
Talla

A kalaman Allegri gabanin fafatawar Juventus da AC Milan jibi Lahadi ya ce dole ne ‘yan wasansa su nuna rawar gani a jibin don kaucewa irin kayen da suka sha a wasansu da Manchester United har gida da ci 2 da 1 a makon nan.

Juventus dai ta sha kwallaye har biyu a hannun Man U ne a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci gab da karkare wasa, wanda kuma shi ne shan kayen karon farko da Club din ya yi cikin sama da watanni biyar inda har dan wasan gaba na Juventus din Cristiano Ronaldo ya ce Man U din ba ta cancanci nasara a wasan ba, kawai dai ta samu sa’a ne.

Yanzu haka dai Juventus ita ke saman teburi a gasar Serie A ta ke kuma da maki 31 tazarar maki 6 tsakaninta da Inter Milan da Napoli wadanda ke matsayin na biyu da na uku yayinda AC Milan ke matsayin ta 4 a teburin na Serie.

A cewar Allegri wanda ke bayani cikin bacin rai game da nasarar ta United, kowanne Club zai iya fuskantar shan kaye amma shan kaye irin wanda suka sha abin takaici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.