Isa ga babban shafi
Wasanni

De Bruyne zai yi jinyar makwanni 6

Dan wasan Machester City Kevin De Bruyne zai yi jinyar makwanni akalla biyar zuwa shida, sakamakon raunin da ya samu a gwiwa.

Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne.
Dan wasan Manchester City Kevin De Bruyne. Reuters/Lee Smith
Talla

De Bruyne ya samu raunin ne yayin wasan kofin Carabao da suka samu nasara kan Fulham da kwallaye 2-0 a jiya Alhamis.

Gaf da za’a kammala wasan ne de Bruyne ya fice daga filin wasa yana dingishi bayan karon da yayi da dan wasan Fulham Timothy Mensah.

Dan wasan na Manchester City bai jima da mumurewa daga raunin da ya samu ba a baya bayan nan, wanda ya tilasta masa jinyar watanni 2.

Sai dai bayan kammala gwaje-gawje, likitoci sun bada tabbacin cewa munin raunin bai kai matakin da za’a yiwa dan wasan tiyata ba, sai dai kawai tsawon lokacin na makwanni biyar zuwa shida da zai shafe yana jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.