Isa ga babban shafi
wasanni

Ba zan horar da Real Madrid ba- Wenger

Tsohon Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya nesanta kansa daga cikin masu gwagwarmayar neman karbar aikin horar a Real Madrid.

Arsene Wenger
Arsene Wenger Reuters/Paul Childs
Talla

A yayin wata ganawa da manema labarai,Wenger mai shekaru 69, ya ce, ba shi da masaniya game da in da zai tsinci kansa a shekara mai zuwa, amma ba zai kasance kocin Real Madrid ba.

Kocin ya bada tabbacin komawa fagen horarwa a 2019, in da yake cewa, yana da cikakken dabaru kuma a shirye yake ya koyar da dabarun na kwallon kafa.

Kawo yanzu Real Madrid ba ta nada koci na din-din-din ba, abin da ya sa Santiago Solari ke ci gaba da zama kocin rikon kwarya.

Solari ya fara jagorantar kungiyar da kafar dama domin kuwa sun doke UD Melilla da kwallaye 4-0 a gasar Copa de Rey.

Solari ya karbi ragamar kungiyar ne bayan ta sallami Julen Lopetegui a ranar Litinin bayan kashin da suka sha a hannun Barcelona a was an El-Clasico.

Karim Benzema da Marco Asensio da Alvario Odriozola da kuma Cristo Gonzalez su ne suka jefa wa Real Madrid kwallayen hudu a zagayen farko na wasan a jiya.

A ranar 5 ga watan Disamba mai zuwa ne, za a gudanar da zagaye na biyu na fafatawar tsakanin Real Madrid da kuma Melilla a Santiago Bernabeu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.