Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta kori kocinta Julen Lopetegui

Real Madrid ta kori kocinta Julen Lopetegui cikin wata sanawar da Kungiyar ta fitar a daren ranar Litinin wadda ke tabbatar da daukar matakin, bayan taron majalisar gudanarwar ta.

Julen Lopetegui, kocin da kungiyar Real Madrid ta kora daga aiki.
Julen Lopetegui, kocin da kungiyar Real Madrid ta kora daga aiki. REUTERS/Andrea Comas
Talla

A halin yanzu Santiago Solari, mai horar da kungiyar aji na biyu, shi ne zai ci gaba da rikon wucin gadi na horar da babbar kungiyar.

A watan Yunin da ya gabata Real Madrid ta zabi Lopetegui a matsayin sabon kocinta, sai dai shan kayen da kungiyar ta yi a wasanni biyar daga cikin 7 da ta fafata a gasar La Liga, ya tilastawa shugabannin kungiyar daukar matakin sallamar kocin kafin lokaci ya kure musu, kamar yadda suka tabbatar cikin sanawar da suka fitar.

A halin yanzu dai Real Madrid tana matsayi na 9 ne a gasar La Liga ta Spain maki bakwai tsakaninta da babbar abokiyar hamayyarta Barcelona.

Lopetegui ya kafa tarihin zama mai horarwa na farko da Real Madrid ta sha mummunan kaye a karkashinsa bayan soma kakar wasa cikin shekaru 70.

Sabon mai rikon kwaryar horar da kungiyar Santiago Solari ne zai jagoranci wasan da kungiyar za ta buga na Copa del Rey da kungiyar Melilla cikin tsakiyar wannan mako, sai kuma yiwuwar jagorantar wasan La Liga da za ta karbi bakuncin Valladolid a gida ranar Asabar.

Tsohon kocin Chelsea Antonio Conte ne ke kan gaba a tsakanin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Lopetegui, sai kuma kocin Belguim Roberto Mertinez da kuma tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar ta Real Madrid Guti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.