Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 16/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 11/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 11/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 16/11 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 16/11 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 11/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 11/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 16/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 11/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 16/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 11/11 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 11/11 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 16/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 11/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 16/11 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 16/11 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 11/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 11/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 16/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Dubban mabiya addinin Islama sun halarci Sallar Janazar Jamal Khashoggi yau Juma'a a masallacin Fatih da ke tsakiyar Birnin Santambul na Turkiyya, ciki har da Iyalansa, 'Yan uwa da kuma sauran magoya baya dama daidaikun musulmi.
Sallar wadda ta gudana ba tare da gawa ba na zuwa ne bayan tabbar da kisan Dan jaridar da kuma lalata gawarsa a Ofishin jakadancin Saudi na Turkiya.

Wasanni

Ronaldo bayyana ainahin dalilinsa na rabuwa da Real Madrid

media Tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo, tare da tsohon mai horar da kungiyar Zinedine Zidane, a lokacin da aka karramasu da da kyautar Ballon d'Or zama gwarzaye kan fannoninsu (na horarwa da kuma kwarewa a fagen fafata wasa). Ben STANSALL / AFP

Cristiano Ronaldo ya ce babban dalilinsa na rabuwa da Real Madrid zuwa kungiyar Juventus shi ne fahimtar da yayi cewa, shugaban kungiyar ta Real Madrid Florentino Perez ba ya ganin kimarsa, kamar yadda yake yi a baya.

Ronaldo ya bayyana haka ne a ganawar da yayi da wata mujallar wasanni ta kasar Faransa, inda ya kara da cewa, bayaga shugaban na Real Madrid wasu daga cikin mambobin kungiyar ma sun daina daukarsa da muhimmanci.

Ronaldo ya ce, ya soma fuskantar rashin bashi kima a Real Madrid bayan shafe shekaru 5 da komawa cikinta bayan rabuwa da tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United.

Yayin hirar da Mujallar wasannin, dan wasan na Juventus ya kara da cewa ajiye aikin horar da Real Madrid da mai horar da shi Zinaden Zidane yayi, ya kara masa kwarin gwiwar rabuwa da kungiyar, domin gwada sa’arsa a wata.

A watan Yulin da ya gabata Ronaldo ya koma Juventus kan kudi euro miliyan 100, bayan shafe shekaru 9 yana hasakawa a Real Madrid.

Tun bayan zartas da matakin rabuwa da Real Madrid da Cristiano Ronaldo yayi, har yanzu kungiyar ta gaza samun dan wasan da zai maye gurbinsa wajen ci mata kwallaye a wasannin da take fafatawa.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure