Isa ga babban shafi
wasanni

Barcelona na ci gaba da jan zarenta a bana

Kungiyar Kwallon Kafar Barcelona ta ci gaba da jan zarenta 100 bisa 100 na buga wasanni ba tare da an doke ta ba a Gasar Zakarun Nahiyar Turai ba, yayin da ta casa Inter Milan da ci 2-0 a fafatawarsu a Camp Nou.

Magoya bayan Barcelona sun jinjina wa bajintar kungiyar a bana
Magoya bayan Barcelona sun jinjina wa bajintar kungiyar a bana REUTERS/Sergio Perez
Talla

Barcelona ta buga wasan ne ba tare da Lionel Messi ba da ke fama da jinyar karayar hannu wadda za ta kai shi ga zaman makwanni kafin komawa fagen tamaula.

Koda yake Messi din ya halarci filin wasan na jiya, in da ya kalli fafatawar daga kan banci.

Rafinha ne ya fara ci wa Barcelonan kwallon farko kafin daga bisani, Jordi Alba ya kara ta biyu.

Ganin karsashin da ta ke nunawa, yanzu haka ana kyautata zaton Barcelona za ta yi bajinta a wasanta na ranar Asabar da Real Madrid, wato fafatawar da ake yi wa lakabi da El-Classico.

A gefe guda dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya jefe kwallaye biyu a fafatawar da suka lallasa Crvena Zvezda da ci 4-0 a gasar ta zakarun Turai.

Yanzu haka Salah ya ci wa Liverpool kwallaye guda 50 a wasanni 65 da ya buga mata tun bayan kulla kwantiragi da ita a bara.

Roberto Firmino da Sadio Mane dukkaninsu sun jefa kwallo guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.