Real Madrid ta sake shan kaye a gasar La Liga
Real Madrid mai rike da kofin gasar zakarun turai, ta sake shan kaye a karo na hudu cikin wasanni biyar da ta fafata a jere, bayanda Levante ta je har gida ta samu nasara kanta da kwallaye 2-1 a gasar La Liga.
Wallafawa ranar:
Rashin nasarar dai ta sanya kungiyar ta Real Madrid kafa tarihin fuskantar koma baya mafi muni a kakar wasa da taba gani, tun bayan shekarar 1985.
Wannan kalubale yasa a halin yanzu, mai horar da kungiyar Julen Lopetegui kara fuskantar matsin lamba fiye da kowane lokaci, ganin cewa a mako mai zuwa Real Madrid za ta fafata wasan El Clasico da babbar abokiyar hamayyarta Barcelona.
A halin yanzu dai Real Madrid ke a matsayin ta 7 a gasar La Liga da maki 14, yayinda abokiyar hamayyarta Barcelona ke jagorantar gasar da maki 18, bayan lallasa Sevilla da kwallaye 4-2.
A baya bayan nan dai, wasu kafafen yada labaran Spain, sun rawaito cewa, akwai yiwuwar Real Madrid ta maye gurbin kocinta Lopetegui da tsohon mai horar da Chelsea Antonio Conte, idan har kungiyar ta ci gaba da fuskantar shan kaye.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu