Isa ga babban shafi
Wasanni

UEFA ta dakatar da kungiyar Kazan tsawon kakar wasa daya

Hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA, ta haramtawa kungiyar Rubin Kazan dake Rasha, buga wasanni har na tsawon kakar wasa guda.

Shugaban hukumar UEFA Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar UEFA Aleksander Ceferin. Reuters / Tony O'Brien Livepic
Talla

UEFA ta ce matakin ya biyo bayan samun kungiyar da laifin kashe kudade fiye da ribar da take samu, wajen sayen ‘yan wasa da kuma sauran al’amura na inganta wasanninta.

UEFA ta soma amfani da tsarin dokar takaita yawan kudaden da kungiyoyi za su iya amfani da su a kakar wasa ne, domin hana attajiran da suka mallaki kungiyoyin amfani da kudi fiye da kima, wajen samun nasarori, abinda ke cutar da kungiyoyin kwallon kafar da basu da kudi.

A karkashin dokokin UEFA, duk kungiyar da aka samu da aikata laifi, za su fuskanci hukunchukuncen da suka hada da takaita cikin ‘yan wasan da suke son yi, takaita yawan ‘yan wasan da za su yi amfani da su a kakar wasa, ko kuma haramta musu buga wasanni zuwa wani wa’adi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.