Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta musanta rahotannin shirin maido da Neymar

Mataimakin shugaban Barcelona Jordi Cardoner, ya ce kungiyar bata da wani shiri ko niyyar sake maido da dan wasanta Neymar da ya sauya sheka zuwa PSG a watan Yuli na shekarar 2017.

Neymar, tsohon dan wasan Barcelona da ya sauya sheka zuwa PSG.
Neymar, tsohon dan wasan Barcelona da ya sauya sheka zuwa PSG. Foto: Reuters
Talla

Cardoner yana mayar da martani ne kan rahoton da wasu kafafen yada labaran Spain suka rawaito dake nuna cewa, Barcelona ta soma shirin ganin da sake maido da Neymar da ta saidawa kungiyar PSG kan farashi mafi tsada a duniyar kwallon kafa na euro miliyan 222.

A cewar mataimakin shugaban na Barcelona, babu koda jami’I daya daga cikin shugabannin kungiyar da ya taba gabatar da tayi maido da tsohon dan was an nasu, ko kuma tattauna kan batun.

Bayan shafe shekaru hudu tare da Barcelona, Neymar ya taka rawa a nasarorin da kungiyar ta samu wajen lashe kofin gasar La Liga 2 da kofin zakarun nahiyar Turai a 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.