Isa ga babban shafi
wasanni

Bolt ya yi watsi da kwantiragin tamaula a Malta

Tsohon gwarzon dan wasan tsere na duniya, Usain Bolt ya yi watsi da kwantiragin da Kungiyar Kwallon Kafa ta Valetta da ke Malta ta ba shi, yayin da zai ci gaba da zama a Australia don cimma burinsa na zama gwarzon dan wasan kwallon kafa kamar yadda wakilinsa ya bayyana.

Usain Bolt na Central Coast Mariners
Usain Bolt na Central Coast Mariners Andrew Murray / AFP
Talla

Tun a cikin watan Agusta ne, Bolt wanda ya lashe kambin gasar Olympic har sau takwas ke kan gwaji a kungiyar kwallon kafa ta Central Coast Mariners da ke buga babbar gasar Lig ta Australia.

Dan wasan ya jefa kwallaye biyu a raga a wata karawar share-fagen kaka a ranar Juma’ar da ta gabata, amma har yanzu Central Coast Mariners ba ta ba shi kwantiragi ba.

Ita kuwa, Valetta ta Malta ta bayyana shirinta na ba shi kwantiragin shekaru biyu kai tsaye ba tare da wani gwaji ba, amma ya bada mata kasa a ido.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.