Isa ga babban shafi
wasanni

Ingila ta doke Spain bayan shekaru 31

A karon farko cikin shekaru 31, kasar Ingila ta doke Spain a wata fafatawa da suka yi a gasar Nations League ta kasashen Turai a Seville.

Lokacin fafatawa tsakanin Spain da Ingila a gasar Nations League
Lokacin fafatawa tsakanin Spain da Ingila a gasar Nations League bibleo.net
Talla

Spain ta sha kashin ne da kwallaye 3-2, in da Raheem Sterling ya zura kwallaye biyu a minti na 16 da kuma 38, yayin da Marcus Rashford ya jefa tasa kwallon a minti na 29.

Ana minti na 58 ne, Paco Alcacer na Spain ya barke kwallo guda kafin daga bisani Sergio Ramos shi ma ya jefa guda a minti na 97.

Raban da Ingila ta samu nasarar akan Spain tun shekarar 1987, lokacin da ta doke Spain da kwallaye 4-2.

Ana kallon wannan nasarar a matsayin mafi kayatarwa da Ingila ta samu a karkashin kocinta, Gareth Southgate.

A karon farko kenan da Sterling ke ci wa Ingila kwallo tun shekarar 2015 kimaninn kwanaki 1102, a yayin wata karawa da Estonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.