Isa ga babban shafi
wasanni

Koscielny ya yi ritaya daga buga wa Faransa tamaula

Dan wasan Faransa da ke taka leda a Arsenal, Laurent Koscielny ya yi ritaya daga buga wasannin kasa da kasa bayan da ya gaza samun damar halartar gasar cin kofin duniya da Faransan ta lashe a Rasha.

Laurent Koscielny a yayin gasar cin kofin duniya ta 2014
Laurent Koscielny a yayin gasar cin kofin duniya ta 2014 REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Koda yake dan wasan mai shekaru 33, ya yi matukar burin halartar gasar ta cin kofin duniya kafin ritayarsa amma aka cire sunansa daga tawagar Didier Deschamps sakamakon raunin da yake fama da shi a kafarsa.

Koscienly ya bayyana bakinsa na rashin kasancewa cikin tawagar Faransa da ta dauki kofin na duniya, in da yake cewa, hakan ya fi bakanta masa rai fiye da raunin da yake fana da shi.

A bangare guda, dan wasan ya soki kocinsa, Deschamps kan yadda ya nuna masa halin ko in kula a yayin da yake zaman jinya, in da ya ce, sau daya tal kocin ya kira sa ta wayar tarho don taya murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa a watan Satumba.

Koscielny ya ce, da dama daga cikin mutane sun yi watsi da shi a yayin zaman jinyarsa.

“ Idan kana cikin yanayi mai kyau, to kana da abokai da yawa, amma idan ka samu rauni, za a mance da kai bayan wani karamin lokaci.” In ji Koscielny.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.