Isa ga babban shafi
Wasanni

Babu tabbas kan wasa tsakanin Saliyo da Ghana

Har yanzu babu tabbas kan yiwuwar wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika tsakanin Ghana da Saliyo, la’akari da cewa har yanzu, FIFA bata amsa wa hukumar kwallon kafar Saliyo bukatar dage haramcin buga wasannin da ta kakaba mata ba.

Kofin gasar kasashen Nahiyar Afrika.
Kofin gasar kasashen Nahiyar Afrika. E.Makundi-RFIkiswahili
Talla

A makon da ya gabata ne FIFA ta haramtawa Saliyo shiga wasanni, saboda abinda ta kira, tsoma bakin da gwamnatin kasar ke yi cikin tafiyar da al’amuran hukumar kula da kwallon kafa ta kasar, lamarin da ya sa aka soke wasan da Saliyo za ta fafata da Ghana a ranakun 11 da kuma 15 ga watan Oktoban da ake ciki.

A ranar Litinin da ta gabata kakakin hukumar wasannin Saliyo Ibrahim Kamara, ya shaidawa manema labarai cewa sun aikewa da FIFA wasikar neman dage haramcin da ta kakaba musu.

Rikicin cikin gidan ya samo asali ne, bayanda hukumar yakar cin hanci da rashawa ta kasar, ta yi yunkurin sauke Isha Johansen da Christopher Kamara, wato shugabar hukumar kwallon kasar ta Saliyo da kuma sakataren hukumar daga mukamansu, bias zargin sun aikata laifukan cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.