Isa ga babban shafi
wasanni

Ko Modric zai iya lashe kyautar Ballon d'Or?

Bisa dukkan alamu Luka Modric da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta FIFA, ka iya sake lashe kyautar Ballon d’Or bayan da aka sanya sunansa a cikin jerin ‘yan wasa 30 da ke takarar lashe wannan gagarumar kyauta a bana.

A ranar 3 ga watan Disamba za a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d'or ta 2018
A ranar 3 ga watan Disamba za a bayyana wanda ya lashe kyautar Ballon d'or ta 2018 REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Modric zai fafata da Cristiano Ronaldo na Juventus da Lionel Messi na Barcelona da Mohamed Salah na Liverpool wajen lashe wannan kyauta.

Modric ya doke Ronaldo da Salah wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan FIFA a bikin da ya gudana a birnin London a watan jiya, in da Messi ya gaza samun shiga jerin ‘yan wasa uku da suka yi fafatawar karshe.

Ronaldo da Messi dukkaninsu sun lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar-biyar, amma a halin yanzu kambun na hannun Ronaldo kafin a samu sabon magaji a ranar 3 ga watan Disamba mai zuwa.

'YAN WASAN DA AKA ZABA DA KUNGIYOYINSU

Sergio Agüero (Manchester City), Alisson Becker (Liverpool), Gareth Bale (Real Madrid), Karim Benzema (Real Madrid), Edinson Cavani (PSG), Thibaut Courtois (Real Madrid), Cristiano Ronaldo (Juventus), Kevin De Bruyne (Manchester City), Roberto Firmino (Liverpool), Diego Godín (Atlético Madrid), Antoine Griezmann (Atlético Madrid), Eden Hazard (Chelsea), Isco (Real Madrid), Harry Kane (Tottenham), N’golo Kanté (Chelsea), Hugo Lloris (Tottenham), Mario Mandzukic (Juventus), Sadio Mané (Liverpool), Marcelo (Real Madrid), Kylian Mbappé (PSG), Lionel Messi (Barcelona), Luka Modric (Real Madrid), Neymar (PSG), Jan Oblak (Atlético Madrid), Paul Pogba (Manchester United), Ivan Rakitic (Barcelona), Sergio Ramos (Real Madrid), Mohamed Salah (Liverpool), Luis Suárez (Barcelona), Raphaël Varane (Real Madrid).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.