PSG a karkashin kocinta, Thomas Tuchel ta zamo kungiya ta farko da ta samu nasara a wasanni tara a jere tun bayan Olympique Lillois wadda ta samu nasara a wasanni takwas a jere a shekarar 1936, kimanin shekaru 82 da suka gabata.
Dan wasan Brazil Neymar ne ya ya jefa kwallo ta biyar a bugun fanaritin da PSG ta samu.
Mbappe ya jefa kwallaye 11 a wasanni 9 da ya buga a wannan kakar wasannin.