Nikolas Vlasic ne ya zura kwallon daya tilo a ragar Madrid kuma dama ya koma CSKA Moscow ne akan aro daga Everton bayan ya buga wasannin firimiyar Ingila har sau 12 ba tare da jefa kwallo ko guda ba.
Karim Benzema da Casemiro da Mariano duk sun yi bakin kokarinsu na ganin sun farke wa Madrid kwallon da aka zura mata.
Sergio Ramos an hutar da shi daga buga wasan na ranar Talata, yayin da Luca Modrid da ya lashe kyuatar gwarzon dan kwallon duniya ke cikin wadanda aka fara ajiyewa a banci.
Gareth Bale bai buga wasan ba saboda raunin da yake fama da shi.
A karon farko kenan da CSKA Moscow ke samun nasara a dukkanin haduwa uku ta yi da Real Madrid a gasar zakarun Turai.
A bangare guda Paulo Dybala ya zura kwallaye uku a karawar da Juventus ta casa Young Boys da ci 3-0 a gasar zakarun Turai,
Wasan na ranar Talata shi ne mafi kayatarwa da Juventus ta yi a kakar nan, amma dan wasanta Cristiano Ronaldo bai buga wasan ba saboda matakin haramta masa wasa guda da UEFA ta dauka sakamakon jan katin da aka ba shi a wasansu da Valencia.