Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya musanta zargin aikata fyade

Cristiano Ronaldo ya sake musanta zargin da wata mata ta yi masa, na cin zarafinta ta hanyar fyade, a wani Otal din Las Vegas dake Amurka a shekarar 2009.

Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal, dake bugawa kungiyar Juventus wasa.
Cristiano Ronaldo dan kasar Portugal, dake bugawa kungiyar Juventus wasa. Marco BERTORELLO / AFP
Talla

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ronaldo, ya jaddada cewa zargin da ake masa karyace kawai da neman bata masa suna.

Dan wasan ya kuma bayyana fyade a matsayin mummunan aikin da ba zai taba goyon bayan mai aikatawa ba.

A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sandan Las Vegas ta sanar da matakin sake bude kundin zargin cin zarafin da aka shigar musu, wanda yayi dai dai da zargin da Kathryn Mayorga, mai shekaru 34 ke yiwa Ronaldo na cin zarafinta a ranar 13 ga watan Yuni na 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.