UEFA ta fitar da jadawalin gasar zakarun Turai na bana
Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin kungiyoyi 32 da za su fafata a gasar lashe kofin zakarun Turai, inda ta rarraba su zuwa rukuni 8.
Wallafawa ranar:
Rukunin farko na jadawalin, wato rukuni A ya kunshi kungiyoyi irinsu Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da Club Brugge.
Sai kuma rukunin B da ya kunshi Barcelona da TOTTENHAM da PSV da kuma Inter Milan.
Akwai kuma rukunin C da ya kunshi PSG da Napoli da LIVERPOOL da kuma Red Star Belgrade.
Yayinda rukunin D ya kunshi kungiyoyi irinsu Lokomotiv Moscow da Porto da Schalke da kuma Galatasararay.
Akwai kuma rukunin E daya kunshi Bayern Munich da Benfica da Ajax da kuma AEK Athens.
Ka zalika rukunin F ya kunshi kungiyoyi irinsu MAN CITY da Shakhtar da Lyon da kuma Hoffenheim.
Rukunin G kuma akwai mai rike da kambu Real Madrid da Roma da CSKA Moscow da Viktoria Plzen.
Yayinda rukunin H kuma ya kunshi Juventus da MAN UTD da Valencia da kuma Young Boys.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu