Isa ga babban shafi
Wasanni

Zai yi wahala Manchester United ta yi abin kirki a bana - Scholes

Magoya bayan Manchester United tare da wasu tsaffin ‘yan wasan kungiyar, suna ci gaba da bayyana rashin kwarin giwar da suke da shi, dangane da samun nasarar United din a kakar wasa ta bana.

Dan wasan Manchester United Scholes lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar  Bolton Wanderers
Dan wasan Manchester United Scholes lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Bolton Wanderers REUTERS/Darren Staples
Talla

Tsohon dan wasan kungiyar na baya bayan nan da yayi tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki shi ne Paul

Scholes, wanda ya ce ba shakka rashin sayen manyan ‘yan wasa sai sa United fuskantar matukar wahala a kokarin ta na lashe kofuna a bana musamman ma na Premier.

Ko a makon daya gabata ma dai kocin kungiyar Jose Mourinho ya koka bisa yadda basu samu nasarra sayen manyan ‘yan wasa ba a kasuwar da aka kare ci, baya ga mai tsaron raga Lee Grant, dan tsakiya Fred da kuma Diogo Dalot.

A makon da ya gabata, dan wasan gaba na Manchester United Alexis Sanchez ya ce tilas kungiyar tasa ta sayo ‘yan wasa kwatankwacin Arturo Vidal da kungiyar Barcelona ta saya a baya bayan nan, idan har tana son lashe kofuna a kakar wasa ta bana.

Sanchez ya bayyana bukatar ce a dai dai lokacin da ake shirin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa, bayan da mai horar da United Jose Mourinho ya bayyana fatan ‘yan wasa biyu daga kungiyoyin Leicester da Bayern Munich, wato Harry Maguire da Jerome Baoteng.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.