Isa ga babban shafi
Wasanni

Subasic ta Madzukic sun yi ritaya daga bugawa kasarsu wasa

Mai tsaron raga na kasar Croatia Danijel Subasic, da kuma dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar kasar Mario Mandzukic, sun sanar da yin ritaya, daga bugawa kasarsu wasa.

'Yan wasan Croatia Mario Mandzukic dan wasan gaba, da kuma Danijel Subasic mai tsaron raga a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow na Rasha, yayin gasar cin kofin duniya ta 2018.
'Yan wasan Croatia Mario Mandzukic dan wasan gaba, da kuma Danijel Subasic mai tsaron raga a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow na Rasha, yayin gasar cin kofin duniya ta 2018. REUTERS/Christian Hartmann/File Photo
Talla

Matakin ‘yan wasan biyu, ya zo ne wata guda bayan rawar da suka taka wajen taimakawa kasar ta su samun nasarar kaiwa matakin wasan karshe na gasar cin kofin duniya ta bana a Rasha, wanda sukai rashin nasara a hannun Faransa da kwallaye 4-2.

Yayin da yake sanar da ritayarsa mai tsaron raga Subasic ya ce ya shirya daukar matakin ne tun kafin soma gasar cin kofin duniya, bayan da ya shafe shekaru 10 yana wakiltar kasarsa.

Shi kuwa Mario Madzukic kafin yin ritaya, sai da ya kafa tarihin zama dan wasa na biyu da fi ciwa Croatia kwallaye baya ga Davor Suker.

A shekarar 2007, Mandzukic ya soma bugawa Croatia wasa, inda zuwa yanzu yake da kwallaye 33 da ya ci wa kasar tasa, a jimillar wasanni 89 da ya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.