Kalaman na Sanchez sun zo ne bayan da United ta sayi sabbin ‘yan wasa biyu, Fred daga kungiyar Shakhtar Donetsk da kuma Diogo dalot daga FC Porto.
Sai dai a gefe guda yayinda aka shiga ranar karshe ta hadar sauyin shekar ‘yan wasa, mai horar da Manchester United Jose Mourinho, na fatan ganin hakarsa ta cimma ruwa, wajen sayen ‘yan wasa masu tsaron baya, Harry Maguire daga Leicester sai kuma Jerome Baoteng na kungiyar Bayern Munich.
A baya bayan nan ne mai horar da Manchester United Jose Mourinho ya ce, kungiyar na fuskantar kakar wasanni mai wahala, muddin bai samu goyon bayan shugabannin kungiyar ba wajen lale kudi don sayen manyan ‘yan wasa.