Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool ta kammala wasanni tunkarar kakar bana cikin nasara

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta kammala wasanninta na tunkarar kakar wasa ta gaba da gagarumar nasara kan Torino ta kasar Italiya da ci 3-1 a filin wasa na Anfield.

Kusan dai dukkanin 'yan wasan na Liverpool dun yi rawar gani musamman a zagayen karshe na wasan.
Kusan dai dukkanin 'yan wasan na Liverpool dun yi rawar gani musamman a zagayen karshe na wasan. REUTERS/Max Rossi
Talla

Liverpool din ce dai ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Firmino a minti na 21 da fara wasa ta kara na biyu a minti na 24 kafin Torino ta zura kwallonta na farko kuma na karshe a minti 31 da fara wasa inda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kuma Liverpool din ta kara a minti na 87.

Wasan na jiya wanda Liverpool ta fara shi da mai tsaron ragarta mafi tsada a duniya Alisson tare da sabbin ‘yan wasa irinsu Naby Keita da Fabinho Xherdan Shaqiri sun nuna bajintar azo a gani

A wasan shima dai Loris Karius mai tsaron ragar kungiyar da ya janyo musu shan kaye a wasan karshe na cin kofin zakarun turai ya yi rawar gani bayan da aka sauya shi da Alisson a zagaye na biyu na wasan.

Tawagar ta Reds ta fara wasannin sada zumuntar ne da Chester wata guda daya gabata kafin daga bisani ta fafata da Tranmere Rovers da Bury dama Blackburn Rovers kafin tafiya Amurka inda ta fafata da kungiyoyi irinsu Brossia Dortmund da Manchester City da kuma United kafin was anta da Napoli a asabar din nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.