Rahotanni na cewa, yarjejeniyar siye kungiyar za ta lakume kimanin Pam biliyan 1 da miliyan 800, kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 2 da miliyan 300
Da ma dai attajirin ya mallaki kashi 67 cikin 100 na hannun jarin Arsenal ta hannun kamfaninsa KSE, yayin da kuma Alisher Usmanov na Rasha ya amince da ya siyar ma sa da kashi 30 da ke karkashin mallakarsa.
Kroenke ya yi amanna cewa, mallakar kungiyar a karkashin mutun guda, za ta taimaka wajen ci gaban kungiyar ta Arsenal.
Kroenke shi ne mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Rams da ke Amurka, yayin da ya fara zuba jari a Arsenal a shekarar 2007, in da kuma yake ci gaba da kara jarinsa kadan-kadan.