Isa ga babban shafi
Wasanni

Berahino ya sauya sheka daga Ingila zuwa Burundi

An tantance dan wasan gaba na Stoke City, Saido Berahino don fara buga wa tawagar kwallon kafar Burundi tamaula bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA ta amince da bukatarsa ta sauya sheka daga tawagar kwallon kafar Ingila zuwa ta Burundi.

Saido Berahino zai sauya sheka daga Ingila zuwa Burundi don ci gaba da buga tamaula a gasa kasa da kasa
Saido Berahino zai sauya sheka daga Ingila zuwa Burundi don ci gaba da buga tamaula a gasa kasa da kasa Reuters
Talla

Dan wasan mai shekaru 25 wanda dan asalin Burundi ne, ya buga wa kasar Ingila kwallo tun daga ajin 'yan kasa da shekaru 16 zuwa ‘yan kasa da shekaru 21, sannan kuma kasar ta nemi ya buga ma ta kwallo a babbar tawagarta a lokacin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin kasashen Turai wato Euro 2016, amma bai samu damar hallara ba.

A can baya, Berahino ya yi watsi da tayin da Burundi ta yi masa na buga mata tamaula duk da cewa, ita ce kasarsa ta haihuwa, amma tun yana dan shekara 10 ya fice daga kasar tare da mahaifiyarsa sakamakon yakin basasa a wancan lokaci, in da suka samu mafaka a Birtaniya.

Yanzu haka ana saran, dan wasan ya fara murza leda a wasan da Burundi za ta yi da Gabon a watan gobe a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.