Jamus ta doke Najeriya a wasan farko na gasar cin kofin duniya
Tawagar kwallon kafar Najeriya ta mata ta Falconets, ta yi rashin nasara a wasan farko da ta fafata tsakaninta da Jamus a gasar ci kofin duniya na mata na ‘yan kasa da shekaru 20, da Faransa ke karbar bakunci.
Wallafawa ranar:
Jamus ta samu nasara kan Najeriya da 1-0 (ci daya mai ban haushi) ne ta hannun ‘yar wasanta Stefanie Saunders a wasan da suka fafata a yau litinin 6 ga watan Agusta, 2018.
Kasashen da Najeriya za ta fafata da su a wasannin gaba na matakin rukuni, sun hada da China da kuma Haiti.
A sauran wasannin da aka fafata a yau Litinin, China ta samu nasara kan Haiti da kwallaye 2-1, sai kuma Spain da ta lallasa Paraguay da kwallaye 4-1.
Sauran sakamakon wasannin da aka yi na farko a ranar Lahadi, sun hada da fafatawa tsakanin Faransa da Ghana, inda ‘yanmatan Faransar suka casa na Ghana da kwallaye 4-1.
Holland kuwa ta samu nasara kan New Zealand da kwallaye 2-1.
Gasar wadda aka soma ta a ranar lahadi 5 ga watan Agusta za ta kare a ranar 24 ga watan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu