Ahmed Musa, joueur de Leicester City
Ahmed Musa, dan wasan Leicester City
Reuters
Dan Najeriya Ahmed Musa da ke bugawa a gasar Premier ta Ingila, ya fice daga kungiyar kwallon kafa ta Leicester City domin kulla sabon kwantaragi da Al-Nassr na kasar Saudiyya.
Musa mai shekaru 25 a duniya, Leicester ta sayo shi ne daga CSKA Moscow a kan fan milyan 16 kimanin shekaru 2 da suka gabata.
To sai dai a wannan karo ba a bayyana adadin kudaden da kulob din na Saudiyya ya biyo domin karbo shi daga Leicester ba.