Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 19/11 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 19/11 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/11 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Wasanni

'Yan kokuwar Najeriya sun nuna bajinta a Algeria

media Wasu daga cikin matasan tawagar da ta wakilci Najeriya a gasar wasannin motsa jikin matasa ta nahiyar Afrika a kasar Algeria.. ACLSports

Shugaban hukumar kula da wasan kokuwa ta Najeriya, Daniel Igali, ya yabawa ‘yan wasan kokuwar da suka wakilci Najeriya a gasar wasannin motsa jiki na matasa ta nahiyar Afrika, da Algeria ta karbi bakunci na wannan shekara.

Yayin wasannin da aka kammala a karshen makon da ya gabata, wato Asabar, 28 ga watan Yuli, 2018, Najeriya ta lashe lambobin Zinare 3, Azurfa 7 da kuma Tagulla 9 a gasar kokuwa kadai, daga cikin jimillar lambobin yabo 103 da kasar ta lashe yayin wasannin motsa jikin, da ta kammala a matsayi na 5.

Lambobin da Najeriya ta lashe a wasanni daban daban da ta fafata a ciki, sun hada da Zinare 29, Azurfa 32 da kuma Tagula 42.

Kasar Masar ce ta lashe gasar wasannin motsa jikin ajin matasa ta bana, bayan lashe jimillar lambobin yabo 199, da suka hada da Zinare 101, Azurfa 55 da kuma Tagulla 43.

Algeria ke biye da Masar da Zinare 71, Azurfa 72 da tagulla 83, jimillar lambobin yabo 226.

Tunisia ke a Matsayi na Uku da Zinare 36, Azurfa 46 da tagulla 54, jimillar lambobin yabo 136, sai kuma Morocco ta kasa ta hudu, da jimillar labobi 106, Zinare 29, Azurfa 37 da Tagulla 40.

A shekarar 2010 aka soma wannan gasa ta wasannin motsa jikin Nahjiyar Afrika ajin matasa, wadda take gudana duk bayan shekaru hudu.

Gasa ta gaba za ta gudana a shekarar 2022, kuma kasar Lesotho ce za ta karbi bakuncinta.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure