Isa ga babban shafi

Dan damben Najeriya ya kalubalanci gwarzayen damben Duniya

Shahararren dan wasan damben Boxing na Najeriya ajin masu nauyi Onoriode Ehwarieme ya ce lokaci ya yi da ya kamata ya fara taro shahararrun takwarorinsa a matakin duniya.

Dan wasan damben Boxing na Najeriya Onoriode Ehwarieme daga bangaren hagu.
Dan wasan damben Boxing na Najeriya Onoriode Ehwarieme daga bangaren hagu. sportingtribune.com
Talla

Onoriode, wanda bai taba shan kaye a sukkanin fafatawar da ya yi a gida Najeriya ba, ya kalubalanci zakaran damben boxing na duniya Anthony Joshua wanda shima bait aba shan kaye ba, da cewa yazo su banbance aya da tsakuwa.

Joshua dai shi ne ke rike da kambun wasannin Damben Boxin na duniya da suka hada da na WBO, IBF da kuma WBA, zalika Joshua ya ci wa Birtaniya lambar Zinari a wasan Boxing da ya wakilce ta na gasar Olympics ta 2012.

Zakaran Damben Najeriya Onoriode ya kuma bayyana cewa a shirye yake, a gefe guda, ya sake fafatawa da Deontay Wilder, wanda shi ma zakara ne a gasar WBC ta Damben Boxing ajin masu nauyi na duniya.

A cewar Onoriode yana da kwarin gwiwar zai iya doke dukkanin zakarun Damben na Boxing Biyu, wato Joshua da Wilder, inda ya ce ai kamata ya yi tun a gasar Olympics ta shekarar 2008 a China ya kamata ya koyawa Joshua hankali, amma sai ya ji tsoro ya ki bayyana a gasar.

A shekarar 2010, Onoriode mai shekaru 30 ya soma wakiltar Najeriya a gasar Boxing a Indonesia ya kuma zama zakara, daga nan ya rankaya Ghana ya lashe gasa, sannan ya sake tsallakawa waje zuwa Argentina a shekarun 2016 da 2017 ya zama gagaraba dau, kafin lashe wata gasar a birnin Lagos na Najeriya.

A shekarar 2008 Samuel Peter na Najeriya, ya taba lashe gasar Damben Boxing na duniya WBC kafin daga bisani Vitali Klitschiko na Ukriane ya karbe kambun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.