Isa ga babban shafi
Wasanni

Ana bincikar mataimakin kocin Najeriya kan cin hanci

Hukumar Kula da Kwallon Kafar Najeriya NFF ta kaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa mataimakin mai horar da ‘yan wasan kasar, Salisu Yusuf kan aikata laifin karbar cin hanci.

Mataimakin mai horar da ‘yan wasan Najeriya Salisu Yusuf.
Mataimakin mai horar da ‘yan wasan Najeriya Salisu Yusuf. Goal.com
Talla

Kaddamar da binciken na zuwa bayan wani faifen hoton bidiyo da wani dan jaridar kasar Ghana ya nuna Yusuf na karbar cin hanci kudi a shekarar da ta gabata, wanda yawansu ya kai akalla Dalar Amurka 1000.

Dan Jaridar mai suna Anas Aremeyaw Anas, ya yi batar da kama kafin tunkarar mataimakin kocin na Najeriya tare da yi mi shi tayin cin hancin domin ya taimaka ma sa wajen sanya sunayen wasu ‘yan wasa biyu a cikin tawagarsa.

Idan za a iya tunawa dan Jarida Anas ne ya bankado badakalar cin hanci da alkalin wasa dan kasar Kenya ya aikata, wato Aden Marwa, wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA ta haramta wa aiki har abada.

Kafin wannan lokacin, tsohon jami’in hukumar CAF da FIFA Amos Adamu, da kuma tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafar Ghana Kwesi Nyantakyi, sun fuskanci hukuncin haramta musu ayyuka daga hukumar ta FIFA, bayan bankado laifukan da suka aikata da suka shafi badakalar cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.