Isa ga babban shafi
wasanni

'Yan wasan da za su yi takarar lashe kyautar FIFA

‘Yan wasan Faransa da suka lashe gasar cin kofin duniya da suka hada da Kylian Mbappe da Antoine Griezmann da Raphael Varane na cikin jerin ‘yan wasa 10 da za su fafata wajen lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta FIFA.

Antoine Griezmann da  Kylian Mbappe dukkaninsu daga Faransa na cikin zaratan 'yan wasa 10 da za su yi takarar lashe kyautar FIFA a bana
Antoine Griezmann da Kylian Mbappe dukkaninsu daga Faransa na cikin zaratan 'yan wasa 10 da za su yi takarar lashe kyautar FIFA a bana REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Kazalika Hukumar Kwallon Kafar ta Duniya, FIFA ta sanya sunayen zaratan ‘yan wasa biyu da suka saba lashe wannan kyauta, wato Christiano Ronaldo da Lionel Messi cikin jerin ‘yan wasan.

Har ila yau, akwai Luka Modric na Croatia da Eden Hazard na Belgium da Kevin De Bryne shi ma daga Belgium da aka zaba cikin wadanda za su yi takarar karbe kyautar.

FIFA ba ta mance da zaratan ‘yan wasa irinsu Harry Kane na Ingila da Mohamed Salah na Masar a cikin masu takarar ba.

Sai dai babu sunan dan wasan Brazil da ke taka leda a PSG, wato Neymar cikin jerin ‘yan wasan.

A bangare guda, kocin Faransa Didier Deschamp da Zinedine Zidane na cikin wadanda za su fafata wajen lashe kyautar gwarzon koci a bana.

Deschamp ya lashe kofin duniya, shi kuma Zidane ya jagoranci Real Madrid wajen lashe gasar zakarun Turai sau uku a jere.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.