Isa ga babban shafi
wasanni

Masu irin shekaruna na komawa China ne- Ronaldo

Gwarzon dan wasan duniya, Christiano Ronaldo ya ce, yana godiya matuka da damar da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta ba shi ta buga ma ta tamaula, lura da cewa, mafi tarin lokuta, 'yan wasa masu yawan shekaru irin nasa na karewa ne a kungiyoyin kwallon kafa na Qatar ko China.

Cristiano Ronaldo ya koma Juventus daga Real Madrid akan Euro miliyan 99.2
Cristiano Ronaldo ya koma Juventus daga Real Madrid akan Euro miliyan 99.2 REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Ronaldo mai shekaru 33 kuma dan asalin kasar Portugal ya koma Juventus ne da ke Italiya akan farashin Euro miliyan 99.2 bayan ya shafe tsawon shekaru tara a Real Madrid.

Dan wasan ya ce, yana fatan ya zama tauraro mai cike da sa’a da zai lashe wa Juventus gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Ronaldo ya ci wa Real Madrid kwallaye 450 tare da lashe ma ta kofunan gasar zakarun Turai guda hudu da kuma La Liga biyu tun bayan da ya koma kungiyar a shekarar 2009 daga Manchester United.

Dan wasan ya kuma jagoranci kasarsa ta Portugal wajen lashe kofin kasashen Turai a shekarar 2016, yayin da ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.