Isa ga babban shafi
wasanni

"Mbappe zai lashe kyautar dan kwallon duniya"

Tsohon dan wasan Ingila Rio Ferdinand ya ce, zaratan ‘yan kwallon duniya wato Christiano Ronaldo da Lionel Messi za su sallama kambinsu ga matashin dan wasan gaba na Faransa, Kylian Mbappe da ya taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Kylian Mbappé ya taimaka wa Faransa lashe kofin duniya a Rasha
Kylian Mbappé ya taimaka wa Faransa lashe kofin duniya a Rasha REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Ferdinand ya ce, nan da wasu ‘yan shekaru masu zuwa, Mbappe zai tsaya akan dandamali don karbar lambar yabo ta Ballon d’Or da ake bai wa dan wasa mafi kwarewa a duniya, kuma Ronaldo da Messi sun shafe tsawon shekaru suna lashe wannan kyauta a tsakanininsu.

Mbappe mai shekaru 19 ya zama matashin dan wasa na biyu a tarihi da ya ci kwallo a wasan karshe a gasar cin kofin duniya bayan Pele wanda ya fara nuna wannan bajintar a shekarar 1958.

Mbappe ya jefa kwallo ta hudu a ragar Croatia a minti na 65 a wasan na karshe a Rasha, yayin da ya lahe kyautar gwarzon matashin dan wasa a gasar cin kofin duniya a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.