Isa ga babban shafi
Wasanni-Rasha

Jerin 'yan wasan da suka samu girmamawa a Rasha

To tuni dai aka bayar da kyaututtukan girmama ga wasu zaratan ‘yan wasa da suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da ta karkare jiya lahadi a Rasha. Jagaba a ‘yan wasan bayan kasar da ta lashe kofin Faransa da Croatia da ke matsayin ta biyu da kuma Belgium a ta 3, akwai Harry Kane dan Birtaniya.

A rukunin ‘yan wasa masu kwallaye bibbiyu ne aka hango keyar ‘yan Afrika, irinsu Ahmad Musa dan Najeriya da Muhammad Salah dan Masar da Khazri dan Tunisa.
A rukunin ‘yan wasa masu kwallaye bibbiyu ne aka hango keyar ‘yan Afrika, irinsu Ahmad Musa dan Najeriya da Muhammad Salah dan Masar da Khazri dan Tunisa. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Dan wasan na Ingila Harry Kane ya lashe takalmin zinare kan kwallaye 4 da ya zura a raga kuma ita ce kyauta mafi daraja bayan kasashe na daya dana biyu da kuma na uku.

Kane dai shi ne dan wasan Ingila na farko da ya lashe wannan kyauta ta takalmin zinare a gasar cin kofin duniya tun bayan Gary Lineker shekaru 32 da suka gabata.

A rukunin ‘yan wasan da suka zura kwallaye hur-hudu a raga kuma akwai Cristiano Ronaldo dan Portugal mai shekaru 33 sai Antoine Griezman na Faransa da Kyllian Mbappe shima dan Faransar sai kuma Danis Cheryshev dan Rasha da Romelu Lukaku dan Belgium.

Rukunin ‘yan wasa masu kwallaye 2 kuma wadanda suma suka samu girmamawar akwai Edinson Cavani na Uruguay da Costa dan Spain da Dzyuba dan Rasha da Hazard dan Belgium da kuma Mandzukic dan Craotia da Mina daga Colombia da kuma Perisic shima dan Croatia.

A rukunin ‘yan wasa masu kwallaye bibbiyu ne aka hango keyar ‘yan Afrika, irinsu Ahmad Musa dan Najeriya da Muhammad Salah dan Masar da Khazri dan Tunisa.

Sauran masu kwallaye bibbiyun akwai kuma irinsu Neymar, da Suares da kuma Modric.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.